A martanin da ya mai da kan zargin mayakansa da hannu a aiwatar da kisan kiyashi kan fararen hula a garin Bentui mai arzikin man fetur a kasar Sudan ta Kudu; Madugun ‘yan tawayen kasar Riek Machar ya yi furuci da cewa yana girmama mutane, kuma mayakansa ba zasu taba kashe ‘yan kasar Sudan ta Kudu ba. Machar ya kara da cewa ya tuntubi kwamandan rundunarsa a garin Bentiu kan zargin, inda ya musanta duk wani zargin hannu a aiwatar da kisan kiyashi kan fararen hula tare da fayyace masa cewa mafi yawan mayakan ‘yan tawayen da suka kaddamar da hari kan jihar ta Unity mutanen wannan yanki ne saboda haka ba zai yiyu su kashe ‘yan uwansu ba.
A nashi bangaren kakakin ‘yan tawayen Sudan ta Kudu Lul Ruai Koang ya kore duk wani zargin hannu a aiwatar da kisan gilla kan fararen hula a garin na Bentiu tare da daura alhakin kisan kan sojojin gwamnatin kasar.
Tawagar Majalisar Dinkin Duniya da ke kasar Sudan ta Kudu dai ta zargi ‘yan tawayen Sudan ta Kudu ne da hannu a aiwatar da kisan kiyashi kan fararen hula fiye da 200 a cikin wani masallaci gami da wasu kiristoci mabiya darikar Catholika da suke cikin wani coci a lokacin da ‘yan tawayen ke fafatukar neman kwace iko da garin Bentui fadar mulkin jihar Unity mai arzikin man fetur a kasar.ABAN